Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargadi Gwamna Ayodele Fayose na jihar Ekiti akan zargin da yayi ma gwamnatin tarayya musamman akan kudaden da aka raba a watan Satumba har Biliyan 389.

LOANS

buhari and fayose

Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Ayodele Fayose

Wannan gargadi ya fito ne daga Garba Shehu, babban maitaimaka ma shugaban kasa akan hudda da jama’a a wata takarda daya saki. Inda ya bayyana cewa maganganun Fayose basu dace ba, duk da cewa haka Fayose yake.

A cewar Nigerian Bulletin, Shehu ya maganta ne bayan da Fayose a bikin Yaye taliban kwallon Ilimi ta Ikere – Ekiti inda ya bayyana cewa ya kamata Shugaba Buhari yazo yayi ma yan Najeriya bayanin gaskiya akan yanayin da tattalin arziki yake ciki.

A wajen ne Gwamna Fayose ya bayyana cewa tattalin arzikin Najeriya zata kare nan da watanni 3 na shugabancin Buhari.

Mai ba shugaban kasan shawara ya bayyana cewa yana nan a rubuce cewa lokacin gwamnatin Jonathan ne aka raba kudade mafi karanci a tarihin Najeriya.

“Akwai bukatar Fayose ya bar sukar Shugaba Muhammadu Buhari kuma ya kama kanshi. Ya kamata ya ringa sanin yanda abubuwa suke ciki kafin yayi magana.” Inji Shehu.

The post Shugaba Buhari Ya Gargadi Gwamna Fayose appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Powered by WPeMatico

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *