– Tsohon Ministan Kasar nan, Femi Fani-Kayode yace gara da Donald Trump ya lashe zaben Kasar Amurka

LOANS

– FFK yake cewa Sabon Shugaban Kasar Amurka ba zai bar Shugaba Buhari ya musuluntar da Kasar nan ba

– Femi Fani-Kayode ya taya Trump murna bayan ya fito daga tsari

Tsohon ministan sufurin jiragen sama na Kasar nan, Femi Fani-Kayode ya fito daga tsari kwanan nan. Bayan fitowar sa, ya taya Sabon Shugaban Kasar Amurka da aka zaba, Donald Trump murnar lashe zaben Kasar. Yace gara da Trump din ya kada Clinton.

KU KARANTA: Asirin Fayose ya tonu

Ko can dai Mista Kayode ya dade yana goyon bayan Trump, ya taba wani rubutu a nan mai suna ‘Trump da kuma Musulunci’ inda yake cewa hamshakin Dan kasuwan nan Donald Trump, zai lashe zaben Jam’iyyar sa ta Republican, kana kuma ya lashe zaben Kasar Amurka inda za su kara da Hillary Clinton.

A wancan lokaci FFK yace: ‘Duk da cewa mutane da dama ba za su yarda da ni ba har a Najeriya, amma na tababa cewa Trump zai lashe zaben Amerika, kuma ina tare da shi. Mu (Yan Najeriya) abin da muke so.

Femi Fani-Kayode yace Trump ba zai kyale a musuluntar da wata Kasa ba ko ya bar masu tsantsenin ra’ayin addini suna abin da suka ga dama. Kayode yace Trump ne maganin Shugaba Buhari.

Femi Fani-Kayode yake kuma cewa Sabon Shugaban ba zai bari a ci gaba da keta hakkin bil adama ba.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

 

The post Ka ji abin da Femi Fani-Kayode ya fada game da Shugaba Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *