– Shugaban majalisan dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki,ya gargadi yan siyasa da kafafen yada labarai akan bin jita jita akan zuwansa fadar shugaban kasa

– Saraki yace ziyarar da ya kai wa shugaba buhari bashi da alaka da bashin $29.9bn da kuma yan siyasa nata maganganu ba gaira ba dalili

Buhari meets Saraki

Shugaban majalisan dattawa,Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya baiwa yan siyasa shawara da kafafen yada labarai cewa su daina yada jita jita akan ziyararsa fadar shugaban kasa da bukatan shugaban ta amsar bashin $29.9bn daga kasar waje.

KUKARANTA:Wasu ma’aurata sun rabu bayan shekaru 19 sai mijin ya aikama da tsohuwar matarsa wannan

Saraki ya bayyana hakan ne ta mai magana da yawunsa,Yusuph Olaniyonu, inda yace dukkan ganawar da yayi da shugaba buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo bashu da alaka da bashin da shugaban kasa ke bukata.

Yace: Kamar yadda na taba fadawa manema labarai, wadannan maganganun siyasa na gurgunta alamurorin kasa . sai ka ji ana maganar gwamnati kaman maganan mutun daya da za’a iya sasantawa tsakanin Saraki da shugaba Buhari.

“Majalisan dokokin tarayya da nike shugabanta ta yanke shawaranta bisa ga hukuncin kasa da yardar majalisa.

A biyo mu a shafinmu na Tuwita @naijcomhausa

The post Bashin $29.9bn: Saraki ya gargadi yan siyasa akan jita-jita appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply