– Manchester United zasu karbi bakunci Arsenal a ranar 19 ga watan Nuwamban nan a Old Traford acigaba da fafata gasar Firimiya da ake bugawa na shekarar 2016|2017, wanda zasu hadu a sati na 12 da far wasan.

LOANS

– Arsene Wenger yayi alkawarin yin musabaha da Mourinho.

– Dan asalin kasar Faransan dai ya samu nasara ne kawai sau daya a wajen abokin gabar nasa, a inda Mourinhon ya lallasashi sau takwas sannan kuma suka buga kunnen doki sau shidda.

Dan gane da mahimmiyar haduwar da zasuyi a ranar 19 ga watan Nuwamban nan mai zuwa a filin wasa na Old Traford, Arsene Wenger din yayi alkawarin yin musabaha da Mourinho idan suka hadu.

vllkyt5f8s88198uq.7171508c

Tsohon kocin Chelsea yana gaisawa da Arsene Wenger.

Sannan dan asalin kasar Faransan ya bayyana Mourinhon a matsayin wanda ya gama gane yadda yan kungiyar nashi suke wasa, wanda hakan yake bashi damar samun nasara akan sa.

Wanda aduk haduwa da sukayi, Wenger ya samu nasara akansa ne sau daya a gasar F.A, a inda Mourinhon ya samu nasara akan sa sau takwas sannan kuma suka yi kunnen doki sau shidda.

KU KARANTA: Ka ji abin da aka yi wa ‘yan Shi’a a Zaria

Inda kocin yace ” ba’a cin m ko yaushe, haka suma muna cinsu, sannan kuma mun buga kunnen doki da yawa. Kuma babu wani babban koci a duniya da ban taba cinsa ba a tsawon zamana da nayi a kungiyar shekara 20. Bazan iya bayyana dangantakar dake tsakanin mu ba. Sai dai abinda na sani shine zai yima kungiyar sa kokari nima zanyima nawa kungiyar kokari”.

Alokacin da aka tambayeshi ko zai gaisa da Mourinho? Sai ya bayyana cewar “mezai hanashi gaisawa nashi, ai yana daga cikin dokar gasar Firimiya”.

Haka kuma ya bayyana cewar babban wasa ne, wanda duk duniya sukeda bukatar su kalla. Saboda haka idan muka samu nasara akan su to babu shakka zamu kara samun karfi sosai.

Ya kara dacewar, “duk da cewar wani nasarar da muke samu a Old Traford yana sanyamu mu samu matsaloli, to amman wannan nasarar idan muka sameta to babu shakka zata kara mana kwarin gwiwa” yaci gaba da cewar ” muna da karfin mu har zuwa wasan zagaye na sha shida ba’a cimuba, duk da cewar wasan mu da Tottenham a gida ya bamu matsala, wanda ya kamata ace mun cisu domin mu samu damar hayewa kan tebur, amman aka samu matsala. Saidai duk da haka babu komai”

” Suma wa’anda suke kan teburin bada wani abu suka tsere mana ba maki uku ne kawai, komai zai iya canzawa da sauri, mun buga wasannin mu guda 11 kuma masu zafi, babu daya daga cikin kulob din daya fita daga cikin neman zama zakara”.

Wenger dai yaki bari Mourinho ya zauna kusa dashi a taro da Sir Alex Ferguson yayi na bayani akan UEFA daya gudana a Nyon da akayi a watan Satumban data wuce. A inda shine yazo dakin taron na karshe kuma manajan na Manchester United din ya bukaci daya zauna a wani wajen daba kowa kusa da Wenger, inda nan da nan Wenger yace baiyarda ya zauna kusa dashi ba.

The post Zan gaisa da Mourinho inji Wenger appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *