– Jam’iyar PDP ta jahar Ondo tana zargin biredin da dan takarar gwamna jam’iyar APC Rotimi Akeredelu yake raba ma jama’a yana da guba                                       

LOANS

– Dan jam’iyar adawa SAN Eyitayo Jegede yana zargin cewa beredin da ake rabawa yana da wani abu da ze sama mutane ciwo

Dan takarar jam’iyar adawa wato PDP SAN Eyitayo Jegede yana zargin cewa buredin da dan takarar jam’iyar APC yake rabawa yana da wata guba da zata iya kawo ciwo ga lafiyar duk wanda ya ci.

vllkyt13985lg70298.e86c617c

Dan haka ya shawar ci mazauna jahar da kada su karba biredin, dan su kare lafiyar su. Saboda yana zargin biredin da wasu kwayoyin cuta da zasu iya saka ma duk wanda ya ci ciwo.

Mr Jegede ya fadi haka ta hanyar Kayode Fashua daraktan yakin neman zaben jam’iyyar PDP cewa masu bincike su auna sun gano biredin na dauke da sinadarin Bromide wanda in kaci ze iya saka maka ciwon ciki ko kansa, kuma ze iya sanadiyar rasa rai.

Sai dai jam’iyar APC sun fito sun musanta haka” sunce basu san ma wanda ya saka a yi biredin ba balanta rabar da shi, kawai suna kokarin bata mana suna ne, kuma su dauke hankalin dan takarar mu SAN Akeredelu kan zaben da yake fuskanta a ranar 26 ga watan Nuwamba 2016, amma haka ba zata cimma ruwa ba inji sakataren yakin neman zabe Akeredelu.

 

The post Zaben jahar Ondo APC suna raba biredi mai guba-Jegede appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *