– Rundunar hadin gwiwa na ta kasashen yankin tafkin Chadi ta ce daruruwan mayakan Boko Haram ne suka mika wuya, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare haren a bangaren Najeriya

– A wata sanarwa da ya aikawa manema labaru kakakin hedikwatar dakarun kasashen yankin tafkin Chadi Kanal Mohammed Dole, yace daruruwan mayakan Boko Haram sun ajiye makamansu suka mika kai

Boko Haram

Kara tsawwala matakan da ake dauka akansu shine ke dalilin fitowar mayakan suna mika wuya, yanzu dai akwai mayaka 240 da suka riga suka mika wuya.

Yayin da a bangaren Chadi mayakan ke mika wuya sai gashi a bangaren Najeriya sai ‘kara kai hare hare suke yi, a cewar Mohammed Dole hakan na faruwa ne a duk lokacin da aka bude musu wuta a wani bangare sai su gudu zuwa wani bangare.

Ku Karanta: Abu 5 da zaku sani game da marigayi Ibrahim Dasuki, na 4 zai baku tausai

Dakta Bawa Abdullahi Wase, na ganin girman filin kasa ne ke haddasawa mayakan dake yankin tafkin Chadi mika wuya, kasancwar sojojin hadin gwiwa sun bude musu wuta babu yadda zasuyi wajen sake komawa wani bangaren.

A wani labarin kuma, Shugaban daya daga cikin bangarorin kungiyar Boko Haram biyu da ake da su a Najeriya ya ce ko da Hillary Clinton Amurkawa suka zaba a zaben shugaban kasa na makon jiya sun yi hasara.

A cikin wani sakon murya da wani makusancinsa ya aiko wa majiyar mu, Abubakar Shekau ya ce a shirye suke su kalubalanci manufofin zababben shugaban na Amurka.

Ya kuma yi Allah-wadai da matakin da ya ce sarkin kasar Saudiyya mai bin tsarin shari’ar musulunci ya dauka na yin maraba da zaben Mr. Trump.

Ya yi amfani da wannan damar wajen daukar alhakin kai munanan hare-hare kan dakarun Najeriya a wasu sassan jihar ta Borno a kwanannan wanda ya hallaka da dama daga cikinsu.

The post Wuya ko da magani ba dadi! Yan Boko Haram na cigaba da mika wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply