Wata Sajent ta hukumar yan sanda ta kasa, Abotie Adesuwa, an kulle ta ofishin yan sanda bayan da ake zargin ta da saida jaririn wata mai tabin hankali mai suna Toyin, bayan da wani mutum ya kawo ta a a ofishin da sagent din ke aiki a unguwar Akinpelu dake Legas. jaridar The Punch ta ruwaito.

LOANS

Rikicin ya tashi ne bayan da Toyin ta dawo ofishin yan sandan a ranar 9 ga watan Nuwamba inda ta bukaci a bata yaririn ta. Sajent din sai ta nuna bata santa ba, wanda ahakn ne ya jaza fada har kuma hukumar ta gudanar da bincike. Daga bayan sai Sagent din ta bayyana cewa ta saida Dan.

Rahoton da Adesina ta shigar a ofishin yan sanda bai nuna cewa Toyin nada ‘Da ba. Ta bayyana cewa ta dauki jaririn zuwa kauyan su dake jihar Edo inda ta saida ‘Dan a fatakwal.

Wata Majiya daga hukumar yan sanda ta bayya a cewa an gano jaririn, sannan kuma wadanda suka saya an kama su.

Joe Offior, jami’i mai hudda da jama’a a hukumar yan sanda Legas ya bayyana ana gudanar da bincike akan alakar Yar sandan da kuma saida jaririn.

The post Wata Yar sanda Ta Saida Jariri appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Powered by WPeMatico

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *