– Hukumar FA ta sake cin Kocin Man Utd tara saboda kalaman sa

LOANS

– FA tace kalaman Jose Mourinh ga Alkalin wasa Taylor sun yi muni

– Ba wannan ne karo na farko da aka ci Kocin tara ba

Kocin Man Utd

Hukumar FA ta Ingila ta sake kuma cin tarar Kocin Kungiyar Manchester United, Jose Mourinho. Hukumar da ke kula da kwallon kafa na Ingila tace kalaman Kocin, Jose Mourinho ga Alkalin ta ba su yi mata kyau ba ko kadan.

Jose Mourinho ya fadi wasu kalamai ne ga Alkalin wasa Anthony Tailor. Hukumar FA tace duk yadda Alkalan suka yi ba za su burge Kocin ba. Anthony Tailor ne ya busa wasan Kungiyar Man Utd da Liverpool inda aka tashi babu ci a Gidan Liverpool.

KU KARANTA: Ya sauka daga kujerar sa

Kocin na Man utd zai biya tarar pound fam 50,000, wanda wannan ba kananan kudi ba ne. Jose Mourinho ya zargi Alkalin da addabar ‘Yan wasan san a Man Utd. BBC ta rahoto a Jiya cewa bayan tarar, an gargadi Kocin da ya bi a sannu.

Ba dai wannan ne karo na farko da Kocin ya saba shiga cikin irin wannan matsalar ba. Ko shin zai gyara?

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

The post Wannan Kocin ya bani appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *