Shugaba Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa ga ‘yan Najeriya dangane da rasuwar sarkin Musulmi murasbus Ibrahim Dasuki, wanda ya rasu a Litinin, 14 ga watan Nuwamba.

The late Ibrahim Dasuki

LOANS

Marigayi Sarkin Musulmi murabus Ibrahim Dasuki

A wata sanarwa da babban mai taimakawa shugaban kan kafofin yada labarai, Alhaji Garba Shehu ya sa hannu a ranar Talata 15 ga watan Nuwamba, shugaba Buhari ya ambata sarakin Muslimi murabus da cewa, shi muryar zaman lafiya ne a lokacin da ya ke raye.

Shugaba Buhari ya kuma yaba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen gina Najeriya ta yanzu.

Sanarwar ta kuma cigaba da cewa, “Shugaba Buhari na mikata ta’aziyyarsa ga kungiyar Jama’atu nasril Islam, da Majalisar Koli da ta kasa kan harkokin Musulunci, dangane da da rasuwar sarkin musulmi murabus, wanda ya bayar da matukar gudunmawa wajen wanzar da zaman lafiya da hakuri da juna a tsakanin kabilu daban-daban na Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Buhari yana cikin tsaka mai wuya dangane da

“Baya ga gudunmawarsa na zamanantar da masarautun gargajiya domin su tafi da zamani, Shugaba Buhari ya yi amanna da cewa, marigayi Ibrahim Dasuki wanda Allah Ya karbi ransa a ranar Litinin, yana mai shekara 93 da haihuwa, ba za’a manta da irin rawar da ya taka wajen samar da tsarin kananan hukumonin da ake da su a yanzu ba.

“Shugaban kasa na jinjina masa da irin muhimmiyar gudunmawar da ya bayar wajen samar da zaman lafiya da cigaban kasa musamman kan jagorantar rahoton da ya haifar da tsarin kananan hukumomin kasar nan a yanzu.

“Shugaban ya kuma yi addu’ar da Allah Ya ba iyalan mai alfarma sarkin musulmin jimirin wannan babban rashi, shi kuma murabus, Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljanna.”    

Tuni dai aka yi jana’izar marigayin bisa a Sakkwwato a inda manyan mutane daga cikin da kuma wajen Najeriya suka halarta.

The post Ta’aziyyar Buhari dangane da rasuwar Ibrahim Dasuki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *