– Reno Omokri ya soki ministan kudi, Kemi Adeosun

– Yace ai rashin kwarewan ta ya jawo tabarbarewan tattalin arziki

Kemi Adeosun

Kemi Adeosun Ministan kudi

Tsohon ma’aikacin tsohon shugaba Goddluck Jonathan ,Reno Omokri ya yi maganganu akan tabararewan tattalin arziki da kuma kare wasu ministocin da Buhari keyi game da rashawa.

Omokri ya bayyana hakan ne ta shafin sada zumuntarsa ta Facebook inda yayi Magana akan tabarbarewan tattalin arziki da kuma yadda ministan kudi bata cancanta da fitar da Najeriya daga halin da take ciki ba.

KU KARANTA: Muhimman labaran karshen makon da ya gabata

Ya kara da bayani akan yadda shugaba Buhari ke kare ministan sufurinsa, Rotimi Amaechi, duk da ikirarin san a yaki da rashawa.

A ranan Lahadi, 23 ga watan Oktoba, omokri yace : wani ya tambayeni ta’arifin tabarbarewan tattalin arziki. Jawabi na, Idan ya maye Ngozi Okonjo-Iweala mai digirgir a ilimin tattalin arziiki daga jami’ar Massachussets Institute of Technology da kuma Kemi Adeosun wacce digri kawai take da shi a fannin tattalin arziki daga jami’ar gabashin landan, sakamakon shine tabarbarewan tattalin arziki.

The post Reno Omokri ya soki shugaba Buhari akan Kemi Adeosun appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Please follow and like us:
error

Leave a Reply