Kafin karshen shekarar 2017 Najeriya za ta soma fitar da shinkafa zuwa kasuwanni kasashen waje a cewar babban bankin Najeriya CBN

– Babban bankin yayi wannan hasashe ne sakamako hasasahen da yayi na yadda tallafin da ya ke bayarwa wajen nomanta na bayar da kyakkyawan sakamako

Shinkafar roba

Babban bankin Najeriya CBN ya ce Najeriya za ta soma fitar da shinkafa domin sayarawa a kasashen waje a karshen shekarar 2017 a cewar jaridar Punch.

Mai rikon mukamin Daraktan yada labarai na Babban Bankin Mista Isaac Okoroafor ne ya bayyana hakan a ranar Talata 29 ga watan Nuwamba a yayin wani taron fadakarwa ga manoman jihar Bayelsa a shirinsa na bayar da rance ga manoma.

Okoroafor ya ce, shirin na babban bankin tuni har ya soma kawo alfanu, a inda ya bayar da rancen da yake yi ga manoma ya sa kasar za ta soma fitar da shinkafar saboda yawanta da ake nomawa.

KU KARANTA KUMA: Kalli shinkafar roba da ya zagaye kasuwanni

Daraktan yana mai cewa, amfanin da aka samu a noman shinkafa a wannan shekara ya zarce yadda aka yi hasashe, kuma idan har aka ci gaba da hakan, babu shakka Najeriya za ta soma cin kasuwar shinkafa a kasashen waje.

Sannan ya kuma ce, “mun yi aikin gwaji a jihar Kebbi da manoma 78,000 a inda kowannensu ya noma a kalla hekta guda, a wannan lokacin ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da shirin a watan Maris na shekarar da ta wuce.

“Ba kawai jihar Kebbi ba, jihar Ebonyi ta shiga cikin shirin a makon da wuce , kuma jihar na shirin bayar da sama da tan milyan 1 da 200,000. Kuma tuni har ‘yan Najeriya sun soma sa a ajiye musu shinkafar domin shagalin bikin Krismeti.

“Kafin karshen shekarar 2017 Najeriya ba kawai za ta magance bukatar shinkafa a cikin gida ba, za mu zarce hakan mu soma fir da ita kasashen ketare.”

The post Najeriya za ta soma fitar da shinkafa waje a 2017 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Leave a Reply