Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma yan fansho cewa zasu dara nan bada dadewa, saboda sabon tsarin da gwamnati take shirya musu zai goge musu hawaye.

Shugaba Buhari da Sharon Ikeazor

Shugaba Buhari da Sharon Ikeazor

Shugaban ya bada tabbacin ne a ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba sa’ailin daya karbi bakoncin shugaban hukumar shirya tsarin biyan yan fansho (PTAD) Uwargida Sharon Ikeazor a fadar gwamnati dake Abuja.

KU KARANTA: Kalli dalibin daya lashe kyaututtuka 19 a jami’a

Shugaba Buhari ya bada umarnin ayi gaggawar kammala aikin tantance yan fansho dake gudana a yanzu haka a duk fadin kasar nan, sai dai shugaba Buhari yace an gudanar da aikin tantancewar ne don gwamnati ta tsaftace tsarin biyan fansho a kasa baki daya.

Yayin da take jawabi, Uwargida Ikeazor ta bayyana cewa hukumar PTAD ba zata yi kasa a gwiwa ba musamman wajen kare hakkokin yan fansho tare da biyansu hakkokin nasu akan lokaci. Daga karshe Ikeazor tace sun samar da wani tsarin da zai kawar da sata da almundahana a hukumar, tare da tabbatar da adalci ga yan fansho.

Mai taimaka ma shugaban kasa a harkokin watsa labarai Garba Shehu ne ya bada wannan sanarwa a ranar Litinin 28 ga watan Nuwamba.

Zaku iya samun labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

The post Mun shirya tsarin da zai goge ma ýan fansho hawaye – Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Leave a Reply