– Tsaffin ministoci 11 karkashin Jonathan zasu koma jam’iyyar APC

– Kari kuma tsohon gwamna Jolly Nyame, Sanata Andy Uba da wasu Sanatoci zasu koma APC

– Wannan shekewa da suke son yi saboda neman sauki ne bias ga bincike ake gudanarwa akansu

Goodluck Jonathan

Rahotanni da ake samu na nuna cewa kimanin ministocin Jonathan 11 ne suke shirin shekewa jam’iyyar APC.

plan b night club logo

Kana kuma tsohon gwamna Jolly Nyame ,Sanata Andy Uba da wasu Sanatocin jam’iyyar PDP zasu koma APC

Game da cewar jaridar Nation, wannan shekewa da sukeyi na daga cikin wata wayo da tsaffin ministocin key i saboda neman sauki bias ga binciken da hukumomin yaki da rashawa keyi.

KU KARANTA: Rikicin kabila ya sabbaba mutuwan mutane 2, gidaje 15 a kone

Rahoton tace shekewa tsohon ministan sufuri,Umar Idris,daga PDP zuwa APC makon da ya gabata somintabi ne , da daman a nan zuwa musamman yankin arewa.

Wata majiya tace: “Wasu daga cikinsu sun fara Magana da wasu kusoshi a gwamnatin Buhar. Suna duba lokacin da zasu sheke ne. amma Umar Idris yayi karfin hali ya sheke makon da ya gabata.

“Ina tunanin basu son suyi asara a yadda abubuwa ke guana. Ya fara bayyana cewa rikicin PDP zai sabbaba kirkiran wata sabuwar jam’iyya.

Wata majiya ta kara da cewa: “Sabanin abinda kuke ji, jamíyyar APC c eke zuwa suna Magana da kusoshi a tsohon gwamnatin Goodluck Jonathan. Wasu daga cikinmu ana tilasta mana mu sheke saboda rikicin da ke faruwa a PDP.

A biyo mu shafinmu na Tuwita : @naijcomhausa

The post Ministocin Jonathan 11 zasu sheke APC appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Leave a Reply