Kungiyar Swansea city sun kori Francesco Guidolin sun nada madadin shi

-An kori Guidolin a matsayin kocin Swansea                                                               – An zabi Bob Bradley a matsayin sabon mai horarwa

 – Kungiyar tana matsayi na 17 a wasa 7 da suka doka a gasar firimiya

Kungiyar Swansea city sun kori Francesco Guidolin, sun maye gurbin shi da tsohon kocin USA Bob Bradley.

Masu kungiyar yan kasar Amurka sun yanke shawarar korar dan kasar Italy bayan doke kungiyar da Liverpool tayi, sai kawai masu kungiyar suka yi gaggawar nada mai maye gurbin shi.

Francesco Guidolin

Francesco Guidolin

Tsohon kocin USA ya hadu da Huw Jenkis, shugaban kungiyar makon da ya gabata kuma ya gana da masu kungiyar Steve Kaplan da Jason Levien.

Bradley wanda yaje horar da kungiyar Le Haure ta faransa a gurbi na 2, ya kayatar gurin tantancewa. Kamar yadda Jenkins yace” Bradley ya kayatar, shine dalilin da yasa mun yanke hukuncin bashi ragamar Kungiyar.

Giggs ma yana cikin wadanda suka zo tantancewar amma baya da wata kwarewa kan aikin.

Swansea city tana matsayi na 17 a teburin firimiya da maki 4 a cikin wasa 17.

The post Kungiyar Swansea city sun kori Francesco Guidolin sun nada madadin shi appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply