Kuma dai: Shugaba Buhari ya kara ganawa da Bukola Saraki

– Shugaba Buhari ya kara wata ganawa da shugaban majalisar dattawa na kasar Bukola Saraki

– Shugaban kasar, Muhammadu Buhari ya gana da Bukola Saraki ne a fadar shugaban kasa Aso Villa

.

Sponsored Video: MUST WATCH! Thanks for watching!

– Kwanakin baya kadan shugaban kasar ya gana da shugaban majalisar kasar

Muhammadu Buhari da Bukola Saraki

Buhari and Saraki

 

 

 

 

 

 

Jaridar Daily Trust tace Shugaba Buhari ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa na Najeriya, Bukola Saraki a Ranar Jumu’a nan. Shugaba Buhari dai yayi ganawar sirri ne, daga shi sai Dr. Bukola Saraki a Ranar 11 ga Wata a Fadar sa.

Ganawar Shugaban Kasar da kuma Shugaban Majalisu na Kasar ya dauki kimanin sa’a guda. Bayan taron kuma Bukola Saraki bai bari yayi magana da ‘Yan Jarida da ke cikin Fadar Shugaban Kasar ba.

KU KARANTA: PDP ta zargi Shugaba Buhari

Ba a dade da Shugaban Kasar ya gana da Bukola Saraki ba, ya kuma gana tare da shi da Mataimakin sa, Ike Ekeremadu. Da alamu dai Fadar Shugaban Kasa na kokari dinke barakar da ke tsakanin ta Majalisar Kasar. Tashin farko dai Majalisa tayi facakalo da rokon Shugaban Kasar na aro kudi har Biliyan kusan $30.

Jaridar The Nation tace abin da aka tattauna ba zai wuce maganar karbo bashin da Gwamnatin Kasar ke kokarin yi ba. Sanatocin Kasar da dama suna kukan Shugaban Kasa ba yayi da su. Sau uku kenan Shugaban Kasar yana zama da Shugaba Majalisar Dattawar Kasar, Bukola Saraki.

The post Kuma dai: Shugaba Buhari ya kara ganawa da Bukola Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Discover Express products online at Jumia Nigeria. Explore a great selection of genuine Express at the best price in Nigeria ✓ Price in Naira ✓ 

Products with Jumia Express logo are items stocked and warehouse by Jumia, it ensures fast shipment and quick delivery. CLICK HERE TO SHOP!