– ‘Yan najeriya sun yi Allah wadai da rundunar sojan kasar, bayan sake kashe wani babban soja da kungiyar ta Boko haram ta yi a  Bita akan hanyarsu ta zuwa jahar Adamawa

LOANS

– Sojan, wanda aka fi sani da Laftanar Kanar BU Umar, mako  uku ke nan da karbar ragamar jagorantar bataliya  ta 114 da ke yaki da Boko Haram

Boko Haram

Abubakar Shekau da kanar Ali da ‘Boko Haram ke ikirarin kashewa

A cewar wasu, ya kamata Buhari ya  kori masu ba shi shawara wadanda ke da hannu a kan badakalar makamai.  A cewar wasu, Shugaban ya  biya wasu makudan kudade domin sako  wasu daga cikin yan matan chibok wanda da su ne Boko Haram ta sayo karin makamai.

Wasu kuwa cewa ke yi, rundunar sojan kasar ce kawai ta ke kashe sojojinta, a yayin da kuma wasu suke ganin cewa rayuwar sojojin  ba ta da wani mahimmanci sosai ga gwamnatin tarayya,

Idris Yusuf Idris, daya daga cikin wanda ya bayyana ra’ayinsa a yanar gizo bayan an buga labarin, ya ce: “Hhhhhhmmmm don Allah yan jaridar Naji.com ina son ku gane, kar ku ce’ yan kungiyar Boko Haram ta kara kashe wani babban soja, kawai ku ce rundunar soja ta kara kashe wani sojanta. Na kasa gane wane irin siyasa a ke yi a kasata Najeriya.”

KU KARANTA KUMA: Shekau ya fito, yace shi ya kashe Abu Ali

Dalibi mai karantar kimiyar siyasa, Philip Chinedu Onwuegbule, ya fusata a lokacin da ya ga rahoton, ya bayyana cewa, “a siyasar Najeriya ne kawai a ke wasa da rayukan bil’adama, kamar yadda ya ba da misali a kan zaben kasar Amurka, “a Najeriya ne kawai a ke siyasar da ake rasa rayuka, kalli yadda zaben America ya gudana, babu wani rahoto na rasa rayuka.

Buhari ya ce, “zai ga bayansu, amma ga shi su na ta kashesu. Mun gode Allah Biafra tana nan, mun sha banban da su,” ya rubuta.

Shi kuwa Junior Chukwuka, cewa ya ke,  ya yarda da cewa Najeriya ba wai tana mutuwa ba ne, ya kuma nuna alhininsa ga sojojin da ‘yan ta da kayar bayan su ka kashe kwana kwanannan.

Wani mazaunin Abuja Alfred Joshua cewa ya ke: “Saboda kawai Buhari ya basu Dala Miliyan 150 don karbar ‘yan matan 29, wadanda ba ma ainihin ‘yan chibook bane, shine su yan boko haram din zasu sayi manyan makamai. Yanzu suna samar da yungurin na huhari na buhari kenan. Shike nan sai su yi ta kashewa da yawa … ai babansu ne akan mulkin.”

Ku ma ku aiko da naku ra’ayin a shafinmu na Facebook ko kuma a Tuwita a @naijcomhausa

The post Kisan wani kwamandan Soja ya janyo ka-ce-na-ce appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *