Shugabannin jam’iyyar PDP sun gudanar da wani taron gaggawa a jiya Alhamis 29 ga watan Oktoba a Abuja. 

Taron dai an gudanar da shi ne domin a fiddo da sabuwar hanyar da za’a bata gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari. Jaridar This Day ta ruwaito.

Shugabannin jam’iyyar PDP da gwamnonin jam’iyyar sun fara halarta wajen ne da kimanin karfe 8 na dare. An fara taron ne da karfe 9 na daren.

Wata makiya daga cikin taron ta bayyana cewa sun gudanar da taron ne nasarar da jam’iyyar APC take samu a kotun zaben. Suna Neman hanya da zasu dakatar da Hakan.

Olisa Metuh a wata takarda daya fitar a ranar 26, ga watan Oktoba yayi Allah wadai akan yadda jam’iyyar APC me amfani da bangaren shari’a wajen amshe mulki jihohi daga hannun su.

A makon daya wuce ne Kotun zabe ta Jihar Rivers ta soke zaben gwamna Wike, Inda tayi umurni da a sake Wani zaben cikin kwana 90. Sannan Kuma Kotun Akwa Ibom itama ta soke zabuka kananan hukumomi 18 Na Jihar ta Akwa Ibom.

The post Jam’iyyar PDP Ta Gudanar Da Taron Gaggawa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *