– Gwamnatin tarayya tayi alkawarin shawo kan matsalolin yankin kudu maso gabashin Najeriya

– Ta nuna damuwarta akan zanga-zangar da akeyi wanda sabbaba zubar da jini

– Gwamnatin tarayya na kira da jamaá su taimaka wajen samar da zaman lafiya

Sojojin Biafra

Akwai rashin kwanciyan hankali a fadar shugaban kasa akan hayaniyar yunkurin samar da yancin Biafra.

Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa zanga-zangar da kungiyar Indigenous People Of Biafra (IPOB) da Movement for the Actualisation for a Sovereign State Of Biafra (MASSOB) key i ya na tayar da hankalin gwamnatin tarayya kuma tayi alwarin magance shi.

KU KARANTA: Wani shugaban makarantar gaba da sakandare ya mutu lokacin da yake lalata da wata

Sakataren gwamnatin tarayya David Babachir Lawal yayi magana ne a bude taron manyan mutane da masana a Abuja inda ya tabbar da cewa gwamnatin tarayya na tattaunawa da masu ruwa da tsaki wajen samar da zaman lafiya a yankin kudu.

Yace gwamnati ta nemi gwamnonin yankin kudu maso gabas su kaddamar da wasu ayyuka da zai taimakawa rayuwan masu zamga-zangan.

Kana David Babachir Lawal yayi Magana akan matsalan garkuwa da mutane inda yace ta dau damara ne daga yankin kudu kafin ta yadu a sauran sassan kasa.

Ya bada tabbacin cewa jami’an tsaro na iyakan kokari wajen dakile ta’addanci.

A biyomu a shafinmu na Tuwita @naijcomhausa

The post FG na bayyana damuwarta game da barazanan ‘yan Biafra appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Leave a Reply