– Dakta Frank Jacobs ya ce Najeriya za ta samu karancin agaji a daga Amurka a zamanin sabon shugaba Trump

LOANS

– Jacob wanda shi ne shugaban kungiyar masu masana’antu ta Najeria MAN ya ce, banbancin alkiblar siyasa na gwamnatocin kasashen biyu zai sa Najeria ta rasa abubuwa da yawa  

Donald Trump

Donald Trump da Buhari

Shugaban kungiyar masu masana’antu na Najeriya MAN, Dakta Frank Jacobs ya ce, sabuwar gwamnatin Amurka za ta rage yawan tallafin da ta ke ba Najeriya a sabuwar gwamnatin Trump mai jiran gado.

Dakta Jacobs ya bayyana hakan ne a yayin wata hira da ‘yan jarida a Abuja a ranar Laraba 16 ga watan watan Nuwamba, ya kuma ce, yana da wahala a yi hasashen yanayin tallalin arzikin kasar idan sabon shugaban kasar Trump ya karbi mulki.

A cewarsa, taimakon da Najeriya ta ke samu daga Amurka na kudi da kuma wasu ayyuka za a janye, saboda sauyin alkiblar gwamnati, da kuma babanci iri na ‘yan jam’iyyar Republicans wacce ta ci zabe a yanzu.

Sannan ya kuma ce, “akwai yiyuwar cewa, Najeriya za ta samu karancin kayyakin tallafi, da karafin gwiwa ta fuskar siyasa… Haka nan wasu tsare-tsare da manufofin jam’iyyar Republican ba za su yiwa bakin haure ‘yan Najeriya da ke Amurka ba dadi ba, daga kalaman yakin neman zaben Trump”.

KU KARANTA KUMA: Trump: Wasu yan Najeriya da suka kama kasa a Amurka

Shugaban kungiyar masu masana’atun ya kara da cewa, ‘yan Najeriya bakin haure a Amurka sun taimaka matuka wajen gina kasar ta fuskar gina tattalin arzikinta a shekaru masu yawa, idan kuwa za su dawo gida, za su iya bayar da babbar gudunmawa wajen gina kasarsu ta gado.

A lokacin yakin neman zabensa shugaba mai jiran gado Donald Trump, ya caccaki shugabannin nahiyar Africa kan yadda cin hanci da rashawa yayi katutu a nahiyar da kuma ci baya, tare da yin tir da tsarin jagorancinsu, ya kuma ba da shawarar da cewa a sake yiwa nahiyar mulkin mallaka.

The post Dangantakar Nigeria da Amurka zai yi tsami -Frank appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *