Shugaba Muhammadu Buhari ya bada kwangilar Dala Biliyan 2.4 domin a gina hanyar jirgin kasa. Kwamishina Sufuri na Legas, Dacta Dayo Maberelola ne ya bayyana haka. Ya bayyana cewa gwamnatocin baya sun gaza wajen bada kwangilar ayi hakan, amma sai yanzu.

LOANS

buhari x

Shugaba Muhammadu Buhari

Sannan kuma ya bayyana cewa suna sa ran za’a gama aikin jirgin kasa na Blue Line a karshen shekara mai zuwa. Da ka daya ya bayyana cewa Legas ita kadai ce jihar da ta dauki wannan aiki ba tare da wani taimako ba daga gwamnatin tarayya. Wanna kudin dala biliyan 2.4 na amfani yan Legas da sauran yan Najeriya ne.

Ya bayyana cewa aikin za’ayi shi a kankanin lokaci. Yace wasu kasashen duk da arzikin su aikin yana daukar su shekaru 7, kamar Dubai.

Idan za’a iya tunawa, Kamfani jirgin kasa na Najeriya, NRC, an fara daura hanyoyin jirgin kasan ne a 1898, sai 1964 Sannan aikin ya kammala. Sannan ya dan tsaya na Wani lokaci kafin a kawo Inginan jirgin Daga kasar waje.

The post Buhari Ya Bada Kwangilar Dala Biliyan 2.4 A Legas appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read on NAIJ.COM.

Powered by WPeMatico

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *