– Wani shaida da aka gurfanar a kan shari’ar Mista Agbele ya tona asirin Gwamna Fayose

merry christmas message from wetinhappen

– Alade Sunday wanda ke aiki a wani banki yace an yi safarar kudin ne ta jirgin sama

– Sannan ya kuma ce asusun Fayose na aiki kafin ya zama gwamna

Da alama Gwamna Ayodele Fayose na cikin babban matsala kamar yadda shaida da aka gurfanar ya bayyana yanda ya karbi kasonsa na cikin dala biliyan 2.1 na kudin siyan makamai.

An ambaci sunan gwamnan cikin bincike da ake gudanarwa kan yadda aka rarraba gudu ta ofishin tsohon mai ba shugaban kasa shawara a harkan tsaro, Sambo Dasuki.

Alade Sunday wanda ya kasance jami’in yarda a wani banki dake Akure, babban birnin jihar Ondo ya bayyana wannan a kotu a ranar Alhamis, 17 ga watan Nuwamba a lokacin da aka gurfanar da Biodun Agbele wanda ya kasance dan kuran gwamnan Ekiti.

Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa a farkon fara shari’ar wanda Justis Nnamdi Dimgba yay i jagora a babban kotun tarayya dake Abuja, shaidan yace an tura  naira miliyan 2.5 zuwa asusun Mista Fayose a ranar 11 ga watan Yuni, na 2014 da kuma miliyan 90 a ranar 23 ga watan Yuni na 2014.

KU KARANTA KUMA: Taiwo Obasanjo tace sabon jam’iyya zai sauya Najeriya

Mike Ozekhome wanda ya kasance mataimaki ga Mista Agbele ya kuma nazarin Sunday wanda ya kara da cewa an biya naira miliyan 1 a asusun Fayose a ranar 2 ga watan Yuni yayinda aka kuma biyan wani naira 895,315 cikin asusun a ranar 5 ga watan Yuni na 2014.

Sannan kuma ya yarda da masu shawara hukumar tsaro na cewa asusun Fayose na aiki kafin ya zama gwamna.

 “An tattara kudin ne a Ghana must go da wani koriyar jakunkuna a cikin jirgin sama.

 “Ya dauke mu tsawon mintuna 45 kafin mu kwashe jakunkunan daga jirgin saman tare da taimakon Olaolu Omotosho, da wasu jami’an tsaro da suka biyo Agbele wanda bazan iya tuna sunansa ba.

 “Bayan mun gama tattaunawa da tsohon karamin minister Musiliu Obanikoro da Agbele a filin jirgin sama, wani Adewale A.O wanda ya bayyana kansa a matsayin ADC na Obanikoro ya raka mu, yayinda Agbele y adage lallai a kirga kudaden.

KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun dakile harin yan kunar bakin wake a Maiduguri, 2 sun mutu

 “Bayan mun gama kidaya kudin ne muka aika su cikin asusu daban daban wanda aka bamu wanda suka hada da na gwamna Fayose.”

Ya kuma bayyana cewa Mista Agbele ya bada umurnin cewa an tafi da wani naira miliyan 263 zuwa Ado Ekiti ko da dai bai bi Olaolu zuwa Ado Ekiti tare da kudin ba.

An daga shari’an zuwa ranar 25, 26 da kuma 27 ga watan Janairu.

The post Badakalar Dasuki: Yadda Fayose ya karbi kason naira biliyan 1.2 – Shaida appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *