– Shugaban hafsan sojoji Janar Tukur Buratai yace yan ta’addan Boko Haram sun sha kashi kuma sojoji na aiki don gannin sun mika wuya a karshe

LOANS

– Buratai yana jin dadi da yanda majalisar dinkin duniya suka taimakawa Najeriya a yakinta na ganin sun kore yan ta’addan Boko Haram daga kasar

Boko Haram

Buratai yace kaso 60 na yan Boko Haram ba yan Najeriya bane

Shugaban hafsan sojin Najeriya Lt. Janar Tukur Buratai ya bayyana cewa yawancin yan kungiyar ta’addan Boko Haram da ke damun Arewa-maso-gabas bay an Najeriya bane.

Jaridar Punch ta hannun News Agency of Nigeria ta ruwaito cewa Buratai ya bayyana hakan a ranar Laraba, 16 ga watan Nuwamba yayinda yake tarban wakilin sakataren majalisar dinkin duniya na musamman Dr. Mohammed Ibn Chambas a hedkwatan Operation Lafiya Dole a Maimalari Cantonment.

KU KARANTA KUMA: Reno Omokri ya kai hari ga shugaba Buhari, EFCC kan Atiku

Ya kuma bayyana cewa yan ta’addan sun sha kashi amma a lura cewa rundunar sojoji zasuji gaba da aiki har sai yan ta’addan sun mika wuya daga karshe.

Buratai ya kuma yi godiya ga majalisar dinkin duniya da suka tuna da Najeriya gurin kokarin ganin sun kora yan ta’addan.

Ibn Chambas yayi amfani da taron gurin yin ta’azziya ga gwamnatin tarayya, sojojin Najeriya, da kuma iyalan marigayi Muhammad Abu-Ali wanda yan ta’addan suka kashe tare da sojoji shidda a ranar 4 ga watan Nuwamba.

A halin yanzu, yan Najeriya sun soki sojojin kasar kan mutuwan wani babban soja wanda yan ta’addan Boko Haram suka kashe a Bita a hanyarsu ta zuwa Yola jihar Adamawa.

The post ‘Ba yan Najeriya bane!’ Buratai ya bayyana abun mamaki game da Yan Boko Haram appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *