img-20161127-wa0000

Wani mutum dan kasar China ya siya mota kirar SUV da tsabar kudi silalla

Hausa news, Wani mutum

A ranar Alhamis 24 ga watan Nuwamba, wani mutum ya futo da tsabar kudi silalla kusan 100,000 domin ya siya sabuwar mota kirar SUV a Henan wato tsakiyar kasar China.

vllkyt46fogfhieol.89e939b5

Mutumin alokacin da yake watsa kudin akan tebur

Andai bayyana cewar mutumin yanada shagon saida kaya ne a birnin Zhengzhou dake Henan Province yadai hada tsabar kudin ne alokacin da baiyi tunanin zai iya samun matsala wajen maidasu kudin takarda ba.

akcarolsfest2016-red

KU KARANTAƘarya ne, ni ba Yesu bane, inji wani Bature

Inda ya bayyana cewar yayi kokarin tuntubar wani bankin dake yankinsu domin su taimaka masa wajen yi mashi canjin kudin zuwa kudin takarda, Amman abin bai yiwuba.

vllkyt5komibh7grm.f9cbf0e7

Wata ma’aikaciyar wajen saida motocin tana kirga kudin da mutumin ya kawo musu domin siyan motar kirar SUV a kasar China.

An dai bayyana cewar, yazo da kudin ne wajen saida motocin inda ya tambayi ko zai iya biyan kudin motar da silallan kudin nasa dayazo dashi? Inda ma’aikaciyar saida motocin ta amince, shine ya futo da kudin ya mika mata. Ya dai dauki ma’aikatana su hudu awa 12 kafin su gama kirga kudin.

Ku biyomu a shafinmu na tuwita. @naijcomhausa

The post Wani mutum dan kasar China ya siya mota kirar SUV da tsabar kudi silalla appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Nigerian newspapers 24/7.

Leave a Reply